Hukumar tsaron farin kaya ta Najeriya, NSCDC a jihar Oyo ta kama wasu mutane biyar bisa zargin hakar ma’adanai ba bisa ka’ida ba.
Kwamandan NSCDC na jihar, Augustine Padonu, ya bayyana cewa an kama wadanda ake zargin tare da manyan motoci guda biyu dauke da kimanin tan 60 na fodar lithium.
Jami’an NSCDC ne suka tare wadanda ake zargin a kofar karban kudi a Ibadan kan babbar hanyar Legas zuwa Ibadan.
Rahotanni sun bayyana cewa an yi lodin ma’adinan ne daga Ilenla da ke Kishi a Jihar Oyo, kuma an nufi siyar da su ne a Jihar Ogun.
Padonu ya lura cewa wadanda ake zargin suna gudanar da ayyukansu ba tare da lasisin da suka dace ba da kuma takardun aikin hakar ma’adinai, sarrafawa, da sufuri.
Za a gurfanar da wadanda ake zargin a gaban kotu da zarar an kammala bincike.
Ya kuma jaddada aniyar hukumar ta NSCDC na kawar da miyagun ayyuka a Oyo sannan ya bukaci jama’a da su ci gaba da samar da bayanai masu amfani don taimakawa wajen tabbatar da doka da oda.