AddiniLabaran Yau

Mijina Ya Takuramun Sai Mun Sadu A Azumi- Ya Zanyi?

Mijina Ya Takuramun Sai Mun Sadu A Azumi- Ya Zanyi?

Malam yau ina cikin damuwa, saboda na kwanta baccin rana, kawai sai na ji mijina ya danne ni, na yi ta kokarin na kwace amma sai ya ci karfina ya sadu da ni, alhalin muna azumi, don Allah malam a taimaka min da mafita, Allah ya sanya wa zuriyarka albarka.

Yer uwa mutukar yadda kika siffanta, haka abin ya faru, to babu kaffara a kan ki, saboda takura miki aka yi, kuma ba ki da laifi a wajan Allah, amma shi kuwa ya saba wa Allah, kuma ya keta alfarmar Ramadana, kuma dole ya yi kaffara, ta hanyar ‘yanta kuyanga, in bai samu ba sai ya yi azumi sittin a jere, in bai samu dama ba sai ya ciyar da miskinai sittin, kamar yadda ya zo a hadisin Bukari mai lamba ta : 616.
Allah ne mafi sani.

DOWNLOAD MP3

Ina Cikin Saduwa Da Mijina A Ramadana Sai Alfijir Ya Keto, Ya Zan Yi?

Malam muna cikin saduwa da mijina a cikin wannan wata, sai muka ji kiran sallar assalatu, me ye hukuncin azuminmu?
To Yer uwa mutukar kuna jin kiran sallar, kun maza da sauri kun datse saduwar da kuke yi, to azumin ku yana nan, amma in har kuka ci gaba da yi koda na second ]aya ne, to azuminku ya karye, kuma za ku yi kaffara ku duka, idan kin yi masa biyayya, in kuma takura miki ya yi, to zai yi kaffara shi ka]ai. Duba Almugni: 3/65.
Allah ne mafi sani.

DOWNLOAD ZIP

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button