Labaran Yau

Ka Kara Albashin Alkalai Ya kai Na Sanatoci, Lauya Ya Fadawa Tinubu

Ka Kara Albashin Alkalai Ya kai Na Sanatoci, Lauya Ya Fadawa Tinubu

Lauyan dokar kasa Dakta Kayode Ajulo ya nemi shugaban kasa Tinubu ya kara Albashin Alkalai ya  kai yawan na sanatocin kasa.

Ajulo ya bayyana hakan ranan litinin a Abuja bayan taya babban Alkalin jihar Ekiti Justice Adedeye jimamin faduwar gini jikin shi wanda ya faru a kotun jiha.

Mista Ajulo ya kara da kiran gwamnati da su kara gina kotun kasa gaba daya, da Kuma inganta albashi da alawus dinsu.

DOWNLOAD MP3

Ya bayyana rashin jindadi akan lamuran albashi da alawus na alkalai, cewa kudin yayi kadan akan sauran jami’un gwamnati wanda ya ta’allaka da Majalisan tarayya da fadar shugaban kasa. Da Kuma aikin da sukeyi ya cancanci karin albashi.

Ya jaddada amfanin karin Albashin Alkalai ya zama daya dana sanatoci, hakan zai kawo adalci a bayanin sa.

“Yana da matukar amfani gwamnati ta kwafan gwamnatin Lagos na canza tsari da yanayin kotu a lokacin mulkin Tinubu a matsayin Gwamna.

DOWNLOAD ZIP

“Wannan aikin yakamata a ayi gaba daya a kasar tunda yanzu yazama shugaban kasa”

Ya kara da cewa yana da kyau a bawa alkalai tsaro, yadda aka kara musu shekarun aiki, kamar na babban Alkalin Osun da gwamnatin jihar.

Ya nemi gwamnatin ta bayyana State of emergency dan kare lafiya da tsaron Alkalai na tarayya dan za a iya musu manakisa.

“Abinda ya faru da babban Alkalin Ekiti ya nuna cewa mafi yawansu alkalai Suna cikin hadari” Cewar sa.

Yace tsaron lafiyar su da dukiyar su ya kamata yazama a gaba, da Kuma gyara Albashi da alawus dinsu.

Alkalai Suna karbar miliyan hudu, duka alkalai na tarayya basu wuce 300 ba amma a Majalisa akwai mutum sama da dari hudu.

Yakamata a daidaita a bayanin sa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button