
Man United Sun Dauko Sofyan Amrabat Da Sagio Reguilon A Matsayin Loan
Fiorentina sun bada Sofyan Amrabat loan akan kudi £8.5m tareda amincewa zasu sayarda Amrabat wa Man United bayan loan dinsa ya kare akan kudi £25m idan Man United suna son ya zauna a kungiyar.

A ranar da za’a rufe Transfer Window, shugaban saye da sayarwa na Man United ya tafi Italy a jirgin sama zuwa wajen da akeyi wa Amrabat binciken lapia domin kammala yarjejeniyar.
Alamu sun nuna zuwan Amrabat Man United kamar cikar burin sa ne, domin ya jima baya training da squad din farko na Fiorentina. Sagio Reguilon ma yazo Man United a loan a free transfer.

Reguilon bai samu buga manyan wasa a Tottenham ba tun April 2022, sanna yaje loan daga Tottenham zuwa Athletico Madrid inda ya buga wasa 11 a gasar Laliga.
Zuwan Reguilon kaman cike matsalolin da Man United suke samu a tsaron gida ne bayan injury da Luke Shaw da kuma Tyrell Malacia suka samu a kungiyar. Yace zai buga duka wani kokarin sa wannan season din a Man United.
Jonny Evans ya saka hannu a kontiraki na shekara daya zuwa Old Trafford.

Evans ya buga wasanni 200 a lokacin da yake Man United, kuma a lokacin yaci Premier League guda 3, gasar kofi guda 2 da kuma Champions League guda daya.