Labaran Yau

Gwamnoni Da Jagororin Kudu Maso Yamma Zasu Gana Da Tinubu Kan Matsalar …

Gwamnoni Da Jagororin Kudu Maso Yamma Zasu Gana Da Tinubu Kan Matsalar Tsaro

“Har yanzu gwamnatin tarayya ita ce hanya daya tilo da za ta iya magance duk wani abun ciki na waje da na cikin gida da ke taimakawa ga wannan matsalar,” Cewar gwamna Uzodinma.

Gwamnonin Kudu maso Gabas da sauran shugabannin kabilar Igbo na shirin ganawa da shugaban kasa Bola Tinubu kan matsalar rashin tsaro a yankin, inji Gwamna Hope Uzodinma na jihar Imo a ranar Jummuat.

Mista Uzodinma ya bayyana haka ne a lokacin da yake zantawa da manema labarai jim kadan bayan ganawarsa da Tinubu a fadar shugaban kasa da ke Abuja.

Gwamnan ya bayyana cewa shi da wasu gwamnonin jihohi biyar na Kudu maso Gabas da kuma shugabannin kungiyar kabilar Igbo, Ohanaeze Ndigbo, sun yanke shawarar ganawa da shugaban kasar kan rashin tsaro a yankin.

Gwamnoni Da Jagororin Kudu Maso Yamma Zasu Gana Da Tinubu Kan Matsalar Tsaro
Gwamnoni Da Jagororin Kudu Maso Yamma Zasu Gana Da Tinubu Kan Matsalar Tsaro

Ya bayyana cewa ya je fadar shugaban kasa ne domin samun ganawa da shugabannin yankin kudu maso gabas da Mista Tinubu.

“Ziyarar ta na da alaka da matsalar tsaro a kasar nan. Yankin Kudu-maso-gabashin kasar nan, ba shakka, kun san an yi ta fama da wannan babban matakin tsaro tun daga ‘yan fashi, da sace-sacen ‘yan bindigar da ba a san ko su waye ba,” inji shi.

Mista Uzodinma ya yi Allah wadai kan yadda matsalar tsaro ta ci gaba da tabarbarewa a yankin duk kuwa da kokarin da al’umma suka yi don dakile lamarin.

Gwamnan ya ce shugabannin za su bukaci shugaban kasa ya ba su goyon baya wajen magance matsalar rashin tsaro a yankin.

A wajen taron, ana sa ran shugabannin Igbo za su ci gaba da neman a sako Nnamdi Kanu, shugaban ‘yan awaren da gwamnatin tarayya ke tuhumarsa da laifin cin amanar kasa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button