Labaran Yau

Majalisar Kano Ta Amincewa Da Sunaye 20 A Matsayin Masu Bawa Gwamna Shawara

MASU BAWA GWAMNA ABBA SHAWARA MUTUM 20 SUN SAMU AMINCEWAR MAJALISA.

Majalisar Kano Ta Amincewa Da Sunaye 20 A Matsayin Masu Bawa Gwamna Shawara

Majalisar Jihar Kano Ta Tabbatar sunayen Masu Bada shawara guda Ashirin wanda gwamna Abba Kabir Yusuf ya nema. 

Shugaban Majalisar Ismail Falgore ya karantawa Majalisan takardan da gwamna ya turo akan tantancewa da tabbatar da su ranan Litinin a Kano.

Bayan zama da sukayi akan takardan a Majalisa, Kuma suka amince da neman tabbacin da gwamna ya Nema.

Falgore yace amincewar yazo ne dan zaban wanda zasu taimakawa gwamna da shawarwari dan kawo dokoki da zata kawo cigaban al’umma da Kuma aiki akai.

Majority leader na Majalisan Lawan Husaini yace zaben Masu Bada shawaran zai taimaka wajen kawo maslaha da Kuma cigaba cikin kankanin lokaci.

“Mai girma gwamna ya turo da takarda wanda ke kunshe da sunaye 20 wanda zasu taimaka masa wajen gudanar da mulkin sa” yayi bayani.

Shi shugaban Majalisan da wasu mambobi yan majalisu sun duba aikin da akayi na kwashe bola da Kuma gyaran asibitocin cikin garin Kano wanda ya bayyana cewa aikin yana kyau.

Ga me da asibitin Hasiya Bayero, Shugaban Majalisar ya ce Sunji dadi da Kuma mamakin yadda mutane suka hallara asibitin dan neman lafiya, hakan ya nuna amfanin sa ga Wa Al’ummar Kano.

Ya bayyana godiyan sa wa Ma’aikatan asibitin wajen yin aiki ba gajiya wa Al’umma, ya Kuma tabbatar musu da cewa Kano zata saka ido kan lafiya a fadin jihar.

Falgore ya yaba wa aikin Hukumar yashe shara da tsaftan gari, wajen kokari da sukayi na fidda sharan da sukayi a cikin kwaryar Kano.

NAN

Join Our:  WhatsApp Group  |  Telegram

Watch African Stories

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button