AddiniLabaran Yau

Yanda Ake Wankan Gawan Mamaci A Musulunci A Saukake

Yanda Ake Wankan Gawan Mamaci A Musulunci A Saukake

In Allah ya dau ran mutum musulmi ya mutu to yana kan yan uwansa ko sauran alummar musulmi da suke wannan wurin da yake dasu mishi wanka, su saka masa linkafani su binne shi yadda addinin musulunci ya kawo.

Ka’idojin Wankan Gawa

Wanda da zai wanke Gawa ana bukatan ya kasance musulmi.
Kuma ya zamto balagaggen musulmi, wanda an shaida gaskiyarsa, amana, adali, wanda aka aminta dashi. Kuma wanda ya san hukunce hukuncen wankan gawa Na musulunci.

Idan Kuma ba a samu na kusa dashi ba wanda ya san hukunce hukuncen wankin gawa ba, Toh Ana bukatar a samo musulmi wanda ya sani dan ya wanke wannan mamacin.

Mai yin wankan gawan ya kasance jinsi daya da mamacin daya mutu, idan namiji ne ya mutu to dan uwansa namiji yayi masa wankan, haka idan macece ta mutu to ya zama mai yi mata wankan yar uwarta mace ne zatayi ba namiji ba. Mata zatayi yiwa mijinta wanka idan ya mutu, haka kuwa miji ya yi wa matarsa wanka idan ta rasu.

Namiji ko mace zasu iya yiwa yara wanda basu wuce shekaru bakwai ba, kuma bai halatta wa musulmi ko musulma su yiwa wanda ba musulmi wanka ba, ko su yi musu jana’iza, ko su yi musu salla, ko su binne su, Duk hakan bai halatta ba.

Idan mace ta yi barin ciki kafin ya cika mutum, ya kai lokacin haihuwa ko an busa masa rai, namiji ne ko mace indai ya kai wata hudu za’a yi masa wanka, ayi masa suttura, ayi masa salla a binne, domin cewa shi bayan wata hudu ya cika mutum.
Ba’a yiwa shahidi wanka, ko salla,balle ma ana binne shi ne da kayansa.

An sako sharudan cewa ruwan da za’ayi amfani dashi ya kasance mai kyau da tsarki, wanda ya kasance a shari’a cewa mai tsarki ne.

Kuma ba a waje bane wanda yake bude, ba a idon mutane ba ko kan hanya, kuma bai halatta ma wanda ba su suke yin wankan ba su je wurin da ake wankan mamacin.

Abubuwan da ake bukata sun hada da shafar hannu, ruwa, sabulu, turare ko camfour, da sauransu.
Kuma Ana so a kula sosai da cuttuttuka da za’a iya shafa daga jikin gawar ko ita gawar ta dauka daga wajen wankan gawar.

Yanda Ake Wankan Mamaci

Ana sanya gawar a waje mai dan tudu kamar kan teburi ko wani abu mai kama da haka da gawar zata zauna da kyau kuma ruwa zai dinga gudana da kyau ya bi ko ina.

Za a cirewa mamacin kayansa, kuma a tabbata an rufe al’auransa da wani yadi ko kaya, a tabbata an rufe alaurar har zuwa lokacin da za a kammala wankan.

Alaurar namiji shi ne daga kan cibiya zuwa gwiwar kafa, mace kuma daga saman kai zuwa gwiwa.
Ana cire duk wani abu daga jikin mamacin, kama daga kan kayansa , zobe, da abubuwan da suka shafi asibiti kamar su allura, robar asibiti, da sauran su.

Gabatar da ruwa mai tsarki mai tsarkakewa.
Mai wankewar ya fara da fadin bismillahi.
Mai wankan ya zauna jikin mamacin dan wanke shi.

Saka hand gloves ko rufe hannu ga wanda zai wanke mamacin, da wannan ne kuma zai wanke duk wani datti daga jikin gawar da ruwa mai tsarki, sannan ya cire hand gloves koh abinda ya sanya hannu sa.

Kuma ya sake saka wata safar ya wanke wajen alaurar mamacin da ita, sai ya yasar

Ana fara wankan da yiwa mamaci alwala ba tare da zuba masa ruwa a Hanci ko bakinsa ba,sai dai za’a iya amfani da tsumma ko cotton wool ko tissue a gogga masa a hakoransa da hanci.
Ana wanke gawar da ruwa da sabulu Idan akwai sabulun.

Bayan an yi alwala irin ta salla, sai a wanke kai wanda ya hada da gashi, fuska, gemu, ga maza, sannan a wanke bangaren saman dama na jikin sannan kuma bangaren saman tsagin hagu, sannan kasan dama sannan na hagu.

Wa gawar mace to ana kwance kitson kanta, a wanke, ayi amfani da comb wajen tace kan, sannan a tattara shi waje ɗaya a kitsa mata guda uku a sako shi bayanta.

Wankan gawan za’a iya yi sau uku ko biyar ko bakwai, iya dai yadda ake so gawar ta wanku, amma da sharaɗin jerantawa wajen wankewar.
A wankewar ƙarshe mai wankan zai iya amfani da camfour (ka fur) ko wani turare acikin ruwan.

Bayan an gama wankan sai ayi amfani da tawul ko wani Zani da za shafe ruwan jikin mamacinmai kyau a tsane gawar, sannan sai a rufe jikin da tsumma mai kyau duk wannan aikin da ake yi a tabbata cewa alaurar mamaci a rufe take. Daga nan sai a shirya saka linkafani.

Ga Karin Bayani Dangane Da Wankan Gawa

Idan gawar ta kasance macece kuma tana cikin haila ta mutu, ko lokacin haiyuwa jini yana zuba to sai a saka pad a tare zuban jinin da yake zuba daga jikinta. Sannan ana so ga wanda yayi wankan gawa shima yayi wanka ko alwala. Sannan babu wata koyarwar musulunci akan yin wasu zikiri ko karatun wasu surori lokacin da ake yin wankan. Kuma ALLAH ne mafi Sani.

Yadda Ake Sakawa Gawa Likkafani

Ana fara yiwa mamaci linkafani da zarar an kammala yi masa wanka, an so ayi amfani da farin tufafi wanda bashi da tsada wajen yiwa gawa linkafani , sai dai babu laifi yi din da wani abu da ba farin yadi ba.

Kuma baya halatta a saka dayawa ba, Ana so a saka daidai wajen sa linkafanin, dukkan awu ya zama dai dai da jikin mamacin. Kuma yadin da za’a yi a, amfani dashi ya kasance babu dinki a jikinsa ko wani zare na siliki ajikinsa ko zaren zinare da sauransu.

Yanda Ake Saka Likkafanin Maza

Linkafanin maza ya haɗa da abubuwa guda uku na farin yadi da igiya guda hudu ta dauri, Yadin waje (lifafah),Yadi na biyu (Izaar),Yadi na uku (Qamees),Zaren kulli guda 3-4.

Zani ƙanana guda 2 satar da za’a yi amfani da su wajen rufe alaurar daya lokacin wanka daya lokacin sa linkafani.

Matakan Sakawa Gawa Likkafani

Yadin rufewar ya zama a buɗe a shimfiɗa su a kasa baki daya, daya a ƙasan ɗaya. Sai a tattaro na farkon daga rabin saman yadin zuwa kai shine Qamees.

Yadin da aka rufe alaurar dashi ana ɗaga shi a sako shi ta bayan mamacin, a saman qamees din.

Ana iya saka turare a wasu daga cikin shashen jikin gawar, wanda sune wuraren sujuda guda bakwai,goshi, hanci, tafin hannaye, gwiwa, da kafa.
Idan da hali za’ayi dora hannun hagun mamacin akan kirjinsa sannan a dora damansa akan hagun, misalin irin yadda ake yi a salla.

Ƙarshen yadin izaar din, ana ɗago shi a nannaɗoshi zuwa bangaren damansa, sannan a naɗo a karashe barin hagu.

Sannan a karshe shine yadin lifafah shima ana nannaɗoshi irin sauran, sannan sai a daure su da zare ko igiya,ɗaya a daure saman kai, ɗaya daga ƙarshen ƙafa, biyu kuma gefe da gefe.

Yadda Ake Sakawa Gawar Mace Likkafani

Linkafanin mata ya hada da abubuwa guda biyar da igiya guda hudu. Linkafanin waje lifafah, Na biyunsa wanda za’a rufe shi daga ƙarƙashin hammata zuwa cinya, Na uku shi ne izaar,Na hudu kuma shi ne qamees, da Na ƙarshe kuma shii ne wanda ake rufe musu gashi da shi.

Yanda Ake Bayyanar Da Rasuwar Mamaci

Ana cewa Inna lillahi wa inna ilayhi raji’un, kamin a bayyana rasuwar musulmi.

Addu’ar Da Akeyiwa Mamaci

Allaahummaghfir li (sunan mamacin) warfa’ darajatahu fil-mahdiyyeena, wakhlufhu fee ‘aqibihi fil-ghaabireena , waghfir-lanaa wa lahu yaa Rabbal-‘aalameena, wafsah lahu fee qabrihi wa nawwir lahu feehi.

Allah yasa mucika da Imani, Aameen.

Karanta Yanda Ake Wankar Gawa

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button