Labaran Yau

Hukumar Yan Kwadigo Ta Kasa NLC Ta Karawa Babban Bankin Sati Biyu Akan Karancin Kudi

Hukumar Yan Kwadigo Ta Kasa NLC Ta Karawa Babban Bankin Sati Biyu Akan Karancin Kudi

Hukumar kwadigo na kasa da Majalisan yan kasuwan Najeriya ta karawa babban bankin kasa CBN lokaci har sati biyu dan ta sake tsabar kudi wa kananan bankuna.

Hukumar da majalisan sun yi zama ne akan in babban bankin bata sake kudade wa kananan bankunan ba har zuwa sati daya 29 ga watan maris, zasu dau mataki tsatstsaura, zasuyi zanga zanga a Ofishin babban bankin kasa na ko wata jiha idan tsabar kudade basu samu ba a kasa baki daya.

Shugaban hukumar kwadigo, Joe Ajaero ya fadawa manema labarai a Abuja kan cewa sunyi yanke hukunci kara lokaci har sati biyu bayan tattaunawa da sukayi da jiga jigan hukumomi da majalisu na yan kasuwa. Saboda sun samu bayanin babban banki tayi kokari sake kudade Duk da kudaden basu dayawa a karona farko na sakewa.

DOWNLOAD ZIP/MP3

Yace zasu bi diddigi da kuma lura da yanda ita babban bankin take fitar da kudin hakan yasa suka kara sati biyun Kamin daukan wani matakin.

Bayan sati biyu daga yau 29 ga watan maris zasu zauna dan su tattauna akan matakin da zasu dauka idan wa’adin sati biyu ya cika, koh hakan zai tallafa wa tattalin arzikin kasa baki daya.

Hukumar Zabe Ta Bawa Gwamnan Kwara Takardan shaidan cin Zabe da wasu 24

Hukumar Zabe a jihar Kwara ta baiwa gwamnan jihar Abdulrazak Abdulrahman da mataimakinsa takardan shaidan zabe da yan majalisun jiha guda Ashirin da hudu.

Anyi taron ne a babban birnin jihar lllorin ranan Talata wanda kwamishinan Zabe Farfesa Sanni Muhammad Adam ya bayar.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button