Jarumar Nollywood Ta Yanke Jiki Ta Mutu A Coci
Likitoci a asibitin East Side a Jihar Enugu sun tabbatar da mutuwar jarumar fina-fina ta Nollywood, Chinedu Bernard.
Jarumar Ta yanke jiki ta fadi ne a yayin da ta ke aikin tsaftace coci na St. Leo the Great Catholic Church da ke rukunin gidajen Tarayya a jihar ta Enugu
A cewar rahoton The Punch, faston cocin, Rabaran Fada Uchendu Chukwuma, da wasu masu ibada a cocin, sun garzaya da ita asibitin a inda aka tabbatar ta rasu.
A cewar wani rubutu da daya daga cikin masu aiki a cocin ya wallafa, ana kokarin tuntubar yan uwanta kafin a kai gawarta dakin ajiye gawa a asibiti.
Jarumar da aka fi sani da Choco ta fito a fina-finai da suka hada da ‘The Mad’, ‘Money Fever’, ‘The Big Mama’s Stick’, ‘The Last Manhood’ da ‘Mad Love’ Da sauransu