Labaran Yau

Yan Bautan Kasa Ta NYSC Mutum Biyar Zasu Maimaita

Yan bautan kasa ta NYSC mutum biyar zasu maimaita

Rifkatu Yakubu, ko’odinatar Hukumar bautan kasa ta Jihar bauchi, ta ce mambobi guda 5 zasu maimaita bautar kasa a jihar Bauchi wanda suka fito a 2022, batch B stream 2.

Ta bayyana hakan wa Hukumar labarai ta kasa a Bauchi ranar Alhamis, wajen karbar takardan shaidan bautan kasa (NYSC certificate) wa mambobin.

Yakubu tace wanda maimaicin ya hau kawunansu dan laifuka ne daban daban wanda ya shafi rashin zuwa da ladabi lokacin bautan kasa.

Ta kara da jaddada cewa Hukumar bara ta lamunci rashin ladabi ba kuma barata sassauta wajen hukunta duk wani mamba ba.

A bayanin ta “Goma daga cikin mambobin za kara musu lokacin bautar kasa na sati biyu, wata daya ko wata uku, saboda sun aikata laifuka daban daban cikin shekarar bautan kasar su”.

Tayi kira ga mambobi da su wuce gidajen su bayan karban takardar shaidan bautar kasa da Kuma su gujewa tafiyan dare.

Ita ko’odinetan ta ce wa wanda zasu maimaita da wanda suka samu karin lokaci da su karasa horaswa na fannin koyon aikin hannu da kasuwanci kamin su gama.

Wanda basu koyi komai ba, ta Basu shawaran suje su koya aikin hannu dan kar su addabi iyayensu.

“Iyayen ku Suna so sugq kuna wani abu komin kankancin shi, yafi zama a gida ba ayin komai.” Cewar Ta.

Daily Nigeria ta rawaito

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button