Labaran Yau

Mutane 14 Neh Suka Rasa Rayukansu A Gagarumin Hatsarin Mota A Hanyar..

Mutum goma sha hudu ne suka rasa ransu a gagarumin hatsarin mota a Bauchi

Mutum goma sha hudu ne suka rasa rayukan su a hatsarin mota da ya faru kauyen Zangoro, dake hanyan Bauchi zuwa Darazo.

Kwamandan Hukumar kula da titi a jihar Bauchi, Yusuf Abdullahi, ya bayyana hatsarin da ya faru ran Alhamis a bauchi.

Yace saura mutum biyar wanda suka samu rauni a hatsarin da ya faru ran Alhamis da misalin karfe 12:17 na rana.

DOWNLOAD MP3

A bayanin shi hatsarin ya faru ne da motar golf wanda ke da rajista AJ507GWA da Kuma wata Chevrolet.

Kwamandan ya bayyana abubuwan da aka samu bayan hatsarin wanda yawon gudu ya kawo, sun hada da naira dubu 73 da wayar salula guda bakwai, power bank guda da kananan jakan hanu guda hudu.

DOWNLOAD ZIP

“Mutum goma sha tara ne sukayi hatsarin, mata goma Sai yarinya mace daya da Yaro na miji daya,Maza baligai goma.

“Mutum sha hudu daga ciki sun rasa rayukan su a lokacin wanda sun hada da mata goma maza biyu Yaro daya yarinya daya”.

Abdullahi ya ce gawawwakin da masu rauni an kai su Abubakar tafawa balewa teaching hospital dake garin Bauchi dan samun kula kamin a samu masu gane su.

Ya shawarci direbobi da su bi dokokin hanya.
Da misalin karfe biyar da rabi na Yamma, Wasu daga cikin gawawwakin an kaisu gwallaga inda aka sallace su.

Ga Bidiyo Daga Bisani ⇓

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button