Labaran Yau

Takaitaccen Tarihin Aishatu Binani | Abubuwan Da Baku Saniba Akan Binani

Takaitaccen Tarihin Aishatu Binani Abubuwan Da Baku Saniba Akan Binani

Aishatu Dahiru Ahmed, wacce aka fi sani da Binani, ‘yar siyasa ce kuma ‘yar kasuwa ce. Wanda a halin yanzu ita ce gomnan jihar Adamawa.

Aishatu Binani ta kafa tarihi a siyasar Nigeria domin itace mace ta farko data fara zama gomnan a Nigeria baki daya.

An haifi Aishatu Binani a ranar 11 ga watan Agusta 1971. Binani ta taba zama ‘yar majalisar wakilai mai wakiltar mazabar Yola ta Arewa/Yola ta Kudu/Girei a a jam’iyyar People’s Democratic Party tsakanin 2011 zuwa 2015.

DOWNLOAD ZIP/MP3

Binani ta yi karatun firamare da sakandare a jihar Kaduna kafin ta wuce Jami’ar Southampton, inda ta samu digiri na uku a fannin Injiniya na Lantarki.

Aishatu Binani ‘yar kasuwa ce domin ita ce ta kafa kamfanin Binani Nigeria Limited, kungiyar Binani Group of Companies da nufin bunkasa da inganta tattalin arzikin yankin Arewa maso Gabas.

Ta fara tafiyar siyasa ne a shekarar 2011 lokacin da aka zabe ta a matsayin ‘yar majalisar wakilai mai wakiltar mazabar tarayya ta Yola ta Arewa/Yola ta Kudu/Girei a jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP).

Daga baya ta sauya sheka zuwa jam’iyyar All Progressives Congress, inda ta lashe zaben kujerar sanata mai wakiltar Adamawa ta tsakiya a zaben 2019.

A matsayin ta na ‘yar majalisar dattijai, Binani tayi aiki a matsayin shugaban kwamitin majalisar dattawa kan muradun ci gaba mai dorewa (SDGs).

Aisha Binani tana auren Farfesa Ahmed Modibbo, kuma sun haihu, kuma Allah ya albarkace su da ‘ya’ya 5

Sanata Aisha Dahiru Ahmed Binani ta lashe tikitin takarar gwamna na jam’iyyar APC a jihar Adamawa inda ta doke maza shida da kuma jiga-jigan siyasa.

Idan mai karatu bai mance ba, a zaben fidda gwanin dai, Binani ta samu kuri’u 430, wanda ya zama mafi rinjaye a zaben, inda ya doke Nuhu Ribadu, tsohon dan takarar shugaban kasa a jam’iyyar Action Congress kuma shugaban hukumar yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa ta EFCC na farko, wanda ya samu kuri’u 288.

Muhammadu Jibrilla Bindow, gwamna mai barin gado ya zo na uku da kuri’u 103, Abdurrazaq Namda ya zo na biyu da kuri’u 94 sai Wafari Theman da 39.

A ranar 14 ga Oktoba, 2022, wata babbar kotun tarayya da ke Yola ta soke takarar Binani a matsayin dan takarar gwamna na jam’iyyar APC a Adamawa.

Kotun, a hukuncin da ta yanke, ta bayyana cewa babu dan takarar jam’iyyar APC a jihar a zaben 2023 amma ta ce masu kara da wadanda ake kara suna da damar daukaka kara kan hukuncin.

Duk da irin wannan kalubalen bai hana ta samun nasara a hankali zaɓen ba, yanzu dai ta faru ta kare Aishatu Ahmad Binani ta zama gomnan jihar Adamawa.

Wannan Shine Tarihin Aisha Binani

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button