Labaran Yau

Yan Sanda Sun Harbe Mutum 4 Cikin ‘Yan Kungiyar IPOB Masu Tilastawa Mutane Zaman….

Yan Sanda Sun Harbe Mutum 4 Cikin ‘Yan Kungiyar IPOB Masu Tilastawa Mutane Zaman Gida A Garuruwan Inyamurai

Rundunar ‘yan sanda a jihar Enugu da ke kudu maso gabashin Najeriya, ta ce ta kashe wasu ‘yan bindiga hudu da ke aiwatar da dokar zaman gida mai cike da cece-kuce na mako guda da wani bangare na masu fafutukar kafa kasar Biafra (IPOB) suka ayyana.

Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Enugu, Daniel Ndukwe ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar a daren Juma’a.

Emma Powerful, mai magana da yawun kungiyar ta IPOB karkashin jagorancin Mista Kanu, Emma ya shaida wa ‘manema labarai cewa su fa suna kan bakar su.

DOWNLOAD HERE

Mista Ndukwe ya ce daga baya ‘yan sandan sun dauko gawarwakin ‘yan bindiga hudu a wani dajin da ke bayan G. Ede Filling Station/Seven-Up, a Awkunanaw, Enugu, inda suka tsere zuwa ciki. Kakakin ‘yan sandan ya ce gano gawarwakin ya biyo bayan wani “tsananin farauta” da hadin gwiwar jami’an tsaro suka kaddamar.

Mista Ammani ya bukaci mazauna yankin da su ci gaba da gudanar da sana’o’insu na halal ba tare da fargaba ba saboda an samar da matakan tsaro domin tabbatar da tsaron lafiyarsu. Kwamishinan ‘yan sandan ya yi kira da a ci gaba da tallafa wa ‘yan sanda da sauran jami’an tsaro wajen yaki da miyagun laifuka a jihar.

DOWNLOAD MP3 HERE

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button