DA ZAFINTA: Hotunan Tsohon Gwamna Fayose Yayin Da Ya Kai Wa Shubagan Kasa Tinubu Ziyara
A ranar Alhamis, 6 ga watan Yuli, tsohon gwamnan jihar Ekiti, Ayo Fayose, ya gana da shugaban kasa, Bola Tinubu a fadar gwamnati dake Abuja, Mai taimaka wa shugaban kasar ya tabbatar da faruwar lamarin a shafin sa na Twitter sannnan ya dora hoton Fayose da Tinubu yayin da suke ganawar, Fayose.
Ya ci gaba da cewa ba shi da shirin ficewa daga PDP ya koma jam’iyyar APC mai mulki
Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu (GCFR) a ranar Alhamis, 6 ga watan Yuli, ya karbi bakuncin tsohon gwamnan jihar Ekiti, Ayodele Fayose a fadar gwamnati dake Abuja.
Duk da cewa ba a bayyana cikakken bayanin ganawar tasu ba amma mai taimaka wa shugaban kasa, kan dabarun sadarwa na zamani, Daddy DO @DOlusegun ya tabbatar da faruwar lamarin a shafin Twitter.
Fayose, bayan ganawarsa da shugaban kasar, ya ce ba zai yi kasa a gwiwa ba wajen caccakar shugaba Bola Tinubu idan ya yi cikakken bayani kan alkawurran da ya yi a yakin neman zabe, kamar yadda tsohon gwamnan Ekiti Fayose ya bayyana
Fayose ya kuma ce ba zai taba barin jam’iyyar PDP ya koma jam’iyyar All Progressives Congress (APC) mai mulki ba.
Fayose ya ce shugaba Tinubu ba masihirci ba ne amma zai iya yin dabara da tawagarsa don sake mayar da kasar nan zuwa mafi kyawu na ci gaban tattalin arziki.
Shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu a jiya ya karbi bakuncin tsohon ministan ilimi, Adamu Adamu a fadar gwamnati dake Abuja.
Adamu ya kasance ministan ilimi na tsawon shekaru 8 a gwamnatin Ba a san cikakken bayanin ziyarar da Adamu ya kai fadar shugaban kasa don ganin Tinubu ba har zuwa lokacin da labaran yau ta hada wannan Rahoton.