Labaran Yau

Daya Daga Cikin ‘Yan Matan Cibok Da Ke Amurka Na Shirin Auren Wani Bature

Daya Daga Cikin ‘Yan Matan Cibok Da Ke Amurka Na Shirin Auren Wani Bature

Joy Bishara, daya daga cikin ‘yan matan makarantar da suka tsere bayan Boko Haram ta mamaye makarantar Sakandaren Gwamnati da ke garin Chibok a Jihar Borno, a shekarar 2014, a kwanan nan ta shiga kasar Amurka.

Kimanin dalibai mata 276 ‘yan shekaru 16 zuwa 18 ne kungiyar Boko Haram ta yi garkuwa da su daga Makarantar Sakandaren Mata ta Gwamnati da ke garin Chibok a Jihar Bornon Najeriya. ‘Yan matan 57 daga cikin ‘yan matan sun tsere nan take bayan faruwar lamarin inda suka yi tsalle daga manyan motocin da ake jigilar su.

Wasu sojojin Najeriya sun ceto wasu amma sama da 100 sun bata.
Sai dai, Bishara da ‘yar uwanta, Lydia Pogu, wadanda ke cikin wadanda suka tsere daga harin da ya dauki hankalin duniya, sun koma Amurka.

Ta gama karatun ta a Jami’ar Kudu maso Gabas, inda ta sami digiri a aikin zamantakewa a 2021.

Ga hotunan Bishara da baturen da take Shirin aure:

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button