Arsenal ta shirya tsaf domin siyan dan wasan gaba na Napoli Victor Osimhen, babban dan wasan gaba na Napoli dan kasar Nigeria, in ji Corriere dello Sport.
Victor Osimhen, mai shekara 25, a shirye yake ya bar Napoli kuma ya zura kwallaye 26 a wasanni 32 da ya yi don taimakawa kungiyar ta lashe gasar Seria A a kakar 2022-23.
Arsenal ta fantama cinikaiyan dan wasan gaban cikin gaggawa dan cika muradin ta na kara karfin gaba. Kungiyar Arsenal tana cikin jerin wanda ake sa musu zaton daukar kopin Premeir League na bana.
Arteta a wani bayanin da yayi, yace a irin wannan yanayi na zafi da kungiyoyin premeir League suka tara, a bune me wahala kayi tasiri in baka da ‘yan wasan gaba daban daban.
Dan wasan na Najeriya dai yana da Yuro miliyan 130, amma Napoli na sane da cewa ba zai rattaba hannu kan sabon kwantaragi ba kuma a shirye yake ya tattauna.
Chelsea, Liverpool, Man United, PSG da kuma dukkanin manyan kungiyoyi a Turai sun bi Osimhen da fatan siyan shi.