Labaran Yau

Hukumar Kidaya Ta Kasa Ta Bayyana Ranar Kidaya

Hukumar Kidaya Ta Kasa Ta Bayyana Ranar Kidaya

Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu zai bayyana sabuwar ranar kidayan mutane da muhalli bayan daga Kidayan kwanakin baya da suka wuce.

Shugaban Hukumar Kidaya ta kasa NPC Nasir Kwarra, ya bayyana hakan ranan Alhamis a gidan gwamnati yayin hira da manema labarai. Bayan sun kai rahoto wanda ya joranci ziyarar da suka kaiwa Shugaban kasa  a fadar sa ta gwamnati Abuja.

Ya ce, kwamishan ta mika wa Shugaban kasa rahoton, Kuma Ana tunanin zai duba Kuma ya fadi ranar da ta kamata ayi aikin a kasa baki daya.

DOWNLOAD MP3

Shugaban Hukumar NPC ya nuna cewa Ma’aikatan zata bukaci kudade masu yawa saboda Duk lokacin da aka kara na kinyi yawan kudi karuwa yake duba da yadda ake samun lamurorin tattalin arziki.

“Munyi Mai bayanin bisa shirin da mukayi na aikin Kidaya, Mun bashi rahoton mafita, Shugaban kasa ya amince da Kuma goyon baya da ya bamu kan Kidaya da shirye shiryenta, ya Kuma kara mana karfin gwiwa wajen shiri.

“Zamu cigaba da shiri kamin muji daga wajen shi ranar da za ayi kidayar, saboda Mun bashi rahoton da zai karanta kamin Ya dawo mana da ansa. Amma akan goyon baya wanda ya bamu, Mun gode masa kuma da ganin amfanin data dan tsare tsare da cigaban kasa” Cewar sa.

DOWNLOAD ZIP

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button