Anfara Gabatar Da Tafsirin Azumin Watan Ramadana Na Bana A Fadar Kano
Ranar Laraba aka fara gabatar da tafsirin Al-qur’ani mai girma na bana, shekarar 2022 da aka saba gudanarwa duk shekara a fadar mai martaba Sarkin Kano, Alh. Aminu Ado Bayero.
Shugaban Darikar Kadiriyya na Afirka, Sheikh Qaribullahi Nasiru Kabara ke fassara, Malam Hadi, ke jan masa bakin Al-qur’anin.
An fara da Fatihatul-Kitab da ayoyin farko na suratu Baqara, inda za a ci gaba da fassara izufi biyu kulum daga jiya laraba zuwa karshen Ramadana.
Tafsirin fadar Kano, tafsiri ne mai dumbin tarihi dadadde da ya kwashe shekaru masu dumbin yawa sama da shekaru 40 ana gabatar da shi a duk shekara a lokacin watan azumin Ramadan.
Sheikh Qaribullah, ya gaji majalasin tafsirin Azumin a wajen mahaifisa, Sheikh Nasiru Kabara, bayan ya shi shehi na Kabaran ya bar duniya a zamanin marigayi mai martaba Sarkin Kano Alh. Dr. Ado Abdullahi Bayero.