Labaran YauPolitics

Hukumar Zabe INEC Zata Bada Takardar Shaidar Zabe Wa Bala Muhammad Kaura Da Yan Majalisu 31 Na Jihar Bauchi Ranan..

Hukumar Zabe INEC zata bada Takardar shaidar Zabe wa Kaura da yan majalisu 31 na Jihar Bauchi ranan Jumma’ah

Hukumar Zabe ta Jihar Bauchi tace, zata bawa Sanata Bala Muhammad da Mataimakin sa Auwal Jatau Takardar shaidan Zabe ran jumma’a.

Hukumar zata bawa yan majalisun Jaha guda talatin da daya Takardar shaidan zabe a jihar bauchi.

Kwamishinan Hukumar zabe ta jihar Bauchi Muhammad Nura ya bayyana hakanne wa jami’an labarai ta kasa a bauchi ran labara, 29 ga watan maris.

Ya jaddada cewa sun bi dokokin yanda hukumar ta zabe ta tanadar na bincike da bada shaidan zabe cikin kwanaki goma sha hudu ma wanda Yaci zabe.

Ya kara da cewa Takardar shaidar zaben za’a bada ne a babban ofishin hukumar zabe dake bauchi.

Gwamna me jiran gado a Kano Abba zai amshi Takardar sa na cin zabe.

A yau Laraba 29 ga watan Maris, Abba kabir Yusuf wanda aka fi Sani da Abba gida gida, ya shirya tsaff domin karban takardar shaidan cin zaben sa a matsayin gwamna a jihar Kano.

Abba ya kasance kwamishinan Ayyuka a gwamnatin Sanata Rabiu Musa kwankwaso a jihar Kano daga shekarar dubu biyu da sha daya zuwa dubu biyu da sha biyar.

Read More

 

DOWNLOAD ZIP/MP3

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button