Labaran Yau

Sojoji Sun Dakile Harin Da Boko Haram Suka Kai A Monguno, Jihar Borno

Dakarun (MNJTF) Operation Hadin Kai sun kashe ‘yan ta’addan kungiyar IS da Boko Haram a yammacin Afrika bayan sun dakile wani hari da suka kai kan al’ummar Monguno a jihar Borno.

An tattaro cewa mayakan na ISWAP a kan manyan motocin hilux da babura sun kai wa sojojin da aka jibge a Marte Axis a Monguno a ranar Asabar 5 ga watan Agusta, wanda ya yi sanadin mumunan artabu na kusan mintuna 30.

Majiyoyin leken asiri sun shaidawa Zagazola Makama, mai sharhi kan harkokin tsaro kuma masani kan yaki da tada kayar baya a yankin tafkin Chadi cewa, sojojin sun yi nasarar dakile harin, inda suka kashe ‘yan ta’addar da ba a tantance adadinsu ba, yayin da wasu suka gudu.

Majiyar ta ce an samu nasarar kwato kayayakin soji daban-daban da suka hada da gurneti yayin da wani soja daya ya samu rauni sakamakon lamarin.

Ku tuna cewa ‘yan ta’addar ISWAP sun sha alwashin kai hari a Monguno duk bayan mako biyu bayan fatattakar su da sojoji suka yi a Monguno.

Join Our:  WhatsApp Group  |  Telegram

Watch African Stories

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button