Labaran Yau

Bazan Karbi Kujerar Minista Ba Ko Da Kuwa Tinubu Ya Bani Cewar Tshon Gwamnan…..

Bazan Karbi Kujerar Minista Ba Ko Da Kuwa Tinubu Ya Bani Cewar Tshon Gwamnan Ekiti Fayose

Tsohon gwamnan jihar Ekiti, Ayodele Fayose, ya bayyana matsayinsa kan nadin ministocin shugaban kasa Bola Tinubu, ya bukaci shugaba Tinubu da ya nada matasa ‘yan kasa da shekaru 65 a matsayin mambobin majalisar ministocinsa, a lokacin da aka tambaye shi ko zai tsallake rijiya da baya na kasancewa daya daga cikin ministocin.

Mambobin majalisar ministocin shugaba Tinubu, tsohon gwamnan ya ce zai ki amincewa da tayin kujerar.

Tsohon gwamnan jihar Ekiti kuma jigo a jam’iyyar PDP, Ayodele Fayose, ya ce zai yi watsi da maganar ko da kuwa anyi masa ita, ko da Bola Tinubu ne yamun tayin da kansa.

Fayose ya bayyana hakan ne a gidan talabijin na Channels TV na shirin dare mai suna Sunday Politics a Abuja ranar Lahadi 9 ga watan Yuli.

A yayin hirar, Fayose ya bayyana cewa ya yi aiki don takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP, tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar ya fadi, inda ya goyi bayan shugaba Bola Ahmed Tinubu.

Sai dai ya ce dalilin da ya sa ya goyi bayan Tinubu ba wai don neman nadin siyasa ba ne kawai don ya yi imani da shi. Da aka tambaye shi ko zai amince da tayin minista daga shugaba Tinubu, Fayose ya ce, “Ba zan taba karba ba,” Ya ce: “Ban taba yiwa PDP aiki a zaben da ya gabata ba. Babu wani dalili da zai sa a ɓoye hakan… Gaskiyar ita ce, na yi aiki da Asiwaju (Tinubu).

Mutum ne mai mutunci daga Kudu maso Yamma. Juyin Kudu ne.”

Ya ce: “Kuna tsammanin zan yi aiki a jam’iyyar da ta dakatar da dana? Jam’iyyar da ta kori dana?
Ya ce tsofaffi sun sace makomar matasa, kuma lokaci ya yi da za a bawa matasa dama.

A halin da ake ciki, Ayodele Fayose ya bayyana abin da zai yi idan shugaba Bola Tinubu ya gaza yin tazarce. Bayan ganawa da Tinubu a gidan gwamnati a ranar Alhamis, 6 ga watan Yuli, Fayose ya ce shi ne zai fara sukar shugaban kasar idan bai cika alkawuran yakin neman zabensa ba.

Tsohon gwamnan ya kuma bayyana cewa ba zai taba ficewa daga jam’iyyar PDP zuwa jam’iyyar APC mai mulki ba duk da cewa yana goyon bayan gwamnatin Tinubu.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button