Kaji tsoron Allah, Kaji tsoron shaidan, kaji tsoron dan PDP cewar El-Rufai
Labarin siyasa ayau shine wata tattaunawa da akayi da mai girma gwamnan kaduna Malam Nasiru Ahmad Elrufai yake cewa anciyo basussuka masu yawa Kuma Ana ayyuka dasu mutane suna gani Dahiru, a cikin bayanin ya hada da cewa inda PDP ne da sun ciyo bashin Kuma sukai Dubai domin siyan gidaje domin shakatawa.
Ya karasa jawabin da cewa su ‘yan PDP sun kasan ce cikin yunwa na shekara takwas, idan har aka basu dama, zasu kwashe kudin ‘kasan Kuma su kwace abubuwan da kuka mallaka. Mal Nasiru yace “kuji tsoron Allah, kuji tsoron shaidan, kuji tsoron dan PDP”.
Jin kadan bada jimawa ba a cikin Kwanakin Nan ne jami’in mu na Labaranyau ya Samu Labarin cewa Gwamnatin Kano Tana Kokarin Rushe Gidan Shahararren Mawakin Siyasan Nan da akafi sani da Dauda Rarara Kahutu.