Labaran YauNEWS

Wannan Harin Farko Kenan, Sakon Rasha

Wannan Harin Farko Kenan, Sakon Rasha

Hukumomin sojojin rasha sunce sun kammala kashi na farko na yakin da sukeyi da kasar Ukraine, yanzu kuma zasu maida hankali kan  yanki Dombass na gabashin kasar, wanda ya kunshi kasashe biyu dasuka balle masu bin tsarin kasan Rasha.

Yankin ya kunshi Donetsk da Luhansk, wadanda ke hannun ‘yan aware masu samun goyon bayan Rasha tun 2014, wadanda kuma a hukumance suke da ‘yancin kansu a wajen Rasha, kafin wannan kutsen da ta fara a Ukraine.

Sai dai kuma a wurin jami’an kasashen Yamma, wannan sanawa na nuna cewa Moscow ta san cewa dabara ko nufinta na kafin ta kaddamar da yakin ya gaza.

A cikin wata daya da ya wuce, dakarun Rasha sun ci gagarumar nasara a wannan yanki, da kuma gefen kudanci wanda ya hada ta da Crimea, tsibirin da shi ma gwamnatin Rasha ta mamaye a shekarar 2014.

Manjo Janar Sergei Rudskoi ya ce Rasha ba ta daina kai hare-hare ba a sauran birane ba, wadanda suka hada da babban birnin Ukraine din Kyiv, amma wannan ba shi ne ainahin babbar manufarta ba.

Wadannan kalamai dai su ne alamu na farko da ke nuna cewa kila Moscow na takaita nufinta na yakin bayan wata daya da kaddamar da shi, inda ta kasa kama ko da wani babban birni daya na Ukraine, kuma hare-haren nata sun gamu da cikas na matsalar kayan aiki da kurakurai da kuma gagarumar turjiya ta Ukraine.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button