Labaran Yau

Kotu Ta Dakatar Da Minista, Hukumar Birnin Tarayya Wajen Rushe Gidajen..

Kotu Ta Dakatar Da Minista, Hukumar Birnin Tarayya Wajen Rushe Gidajen Trademore Estate

Kotun Gwamnatin Tarayya (federal high Court) ta dakatar da Ministan Birnin Tarayya Abuja da Hukumar birnin tarayya FCTA daga rushe gidajen Trademore Estate na Lugbe Abuja.

Justice Zubairu Mohammed ranan laraba ya bayyana wa Ministan da Hukumar cewa da su dakatar da rushe gine ginen wanda suke so suyi
Na fuloti 1981 na sabon Lugbe Abuja bayan bada takardan tashi wa muzauna wajen.

Cikin Hukumar da aka dakatar sun hada da Abuja Metropolitan Management Council (AMMC) da Kuma Abuja Municipal Council (AMAC).

DOWNLOAD MP3

Mai Shari’ar ya bada odar bayan sauraron karar da Benson Igbanoi yayi da Mike Ozekhome (SAN) na Trademore International holdings Nigeria Limited.

Masu karar sun nemi kotu ta bada yancin mallakar gidaje kamin a gama Shari’ar kamin a yi maganar takardan tashi.

An samu bayanin rushe gidajen Trademore estates na Abuja saboda ambaliyar ruwa wanda ya kawo salwantar dukiya da Kuma rasa rayukan mutane.

DOWNLOAD ZIP

Kotu Ta daga zaman zuwa ranan 22 ga Satumba.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button