EntertainmentLabaran Yau

Inajin Dadin Fitowa A Rol Din Muguwa- Jaruma Saratu Gidado

Inajin Dadin Fitowa A Rol Din Muguwa- Jaruma Saratu Gidado


Matakin da fitacciyar jaruma Saratu Gidado take fitowa a matsayin muguwa a cikin fim shi ne ya ke zuwa zuciyar mutane a duk lokacin da aka ambace ta, domin kuwa tun daga lokacin da ta fara harkar fim da wannan rol din ta yi suna don haka ma ko a kan hanya aka gan ta to irin wannan kallon a ke yi mata. Wani abin mamaki da jaruma Saratu Gidado take da shi za a iya cewar ta rike Kambun ta domin tsawon lokacin da ta shafe ana damawa da ita, har yanzu jarumar ana yayin ta, sai dai har yanzu da dama mutane ba su san wacece Saratu Gidado ba, kuma ya aka yi ta samu sunan Daso.

Da Aka tambayeta ta bakinta ko ya takeji Fitowarta koda yaushe a Rol Din Mugunta Sai Tace,

DOWNLOAD MP3

To gaskiya ba zabi na ba ne, don ba zan manta ba, wanda ya fara ba ni wannan rol na mugunta shi ne Darakta Aminu Muhammad Sabo Allah ya ji kan sa, shi ne duk wani fim da zan yi musu, sai ya ba ni rol na mugunta Amma dai ban san dalilin ba ina ganin ko ya fi ganin na fi dacewa da wannan rol din ne shi ya sa ya ke ba ni. Amma dai iyawa ma tana sa a ba ka rol, domin ba kowa zai iya ba, don akwai wadanda idan an ba su daga sun fara sai su kasa to ina ganin yanayi na ya duba shi ya sa ya ke ba ni rol din.

Acewarta Tana Matuqar jin dadin wannan roll din don ta kware kwarai da gaske,  wanda kaman yabi jikinta a harkar tasu,  saidai tace hakan yayi hannun riga da halinta na zahiri.

Samm ita ba muguwa bace,  hasalima akwaeta da son Jama’a sabanin yanda mutane suke mata fassarar fim.

DOWNLOAD ZIP

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button