AddiniLabaran Yau

Hukunce Hukuncen Da Yakamata Kasani Kafin KaYi Aure

KAFIN KAYI AURE KASAN WADANNAN HUKUNCIN KUWA??

Wace mace ya kamata ka aura?? Ke kuma wane namiji ya kamata ki aura a ka’ida ta Shari’a??

Wace hanya ake bi Dan tantance mace a Addini?? Kuma wace hanya akebi Dan tantance miji a ka’ida ta Shari’a??

Shin kasan menene Aure kuwa?? Kasan kuma menene manufa da hikimar yin Aure??da Sharadan yin Aure??

Misali:

Aure baya yiwuwa sai da dayan abubuwa guda 4 Waliyyi , Shaidu , Sadaki ,Siga. Shin kasansu kuwa??

Hakkin miji akan matarsa da Hakkin mata akan mujinta a shari’a ka sansu??

Idan rikici ko rashin jituwa ya faru tsakanin ma’aurata wace hanya akebi Dan warware matsalar a ka’ida ta Shari’a??

Idan ya kama miji zai Saki matarsa wane matakai ake bi ??
Shin yaya ake sakin??menene ka’idojin Saki da Hukuncin sa a Shari’a??

Idan aka Saki mace yaya zata yi kuma yaya zata yi Iddar ta da Sharadan yin Iddar??

Yaya miji zai komo da matarsa?? Kuma ya ake komen??

Dukka wadannan Tambayoyi ya kamata ace mace da Namiji sun sansu kafin yayi Aure.

Allah Ubangiji ka haɗa mu da abokan rayuwa nagari.

#SheikhImamAbubakarBalaGana (Hafizahullah)

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button