A garin Lere da ke karamar hukumar Tafawa Balewa a jihar Bauchi, rahotanni sun ce sojoji daga ‘Operation Safe Heaven’ sun kashe wani matashi mai suna Habibu Aminu tare da raunata wasu hudu a wata arangama da matasan yankin.
Aminu wanda ya kammala hidimar matasa na kasa ya rasu ne a lokacin da sojoji suka kai samame gidajen mutanen da rikicin ya rutsa da su a babban shingen binciken garin.
Rikicin ya faru ne a ranar Talata tsakanin magoya bayan jam’iyyar PDP da suka dawo daga yakin neman zaben kananan hukumomi.
Daya daga cikin wadanda suka jikkata, Babawo Lauwawu, ya ce lamarin ya fara ne lokacin da sojoji suka fara aiwatar da dokar hana fita, wadda aka sanar da karfe 10 na dare.
Shi da wasu sun riga sun shiga gidajensu da karfe tara na dare, amma sun ji karar harbe-harbe kafin a fara dokar hana fita. An harbe Lauwawu a kafa a cikin hargitsi kuma bai fahimci dalilin harbin ba duk da bin bin umarninsu.
Rundunar ‘yan sandan jihar Bauchi ta tabbatar da faruwar lamarin tare da bayyana cewa za a hukunta jami’an da suka aikata laifin. An tura wata tawagar jami’an tsaro da za ta binciki lamarin sosai.
Kwamishinan ‘yan sanda, Auwal Musa Mohammed, ya bayar da tabbacin cewa za a gudanar da cikakken bincike da kwararru domin tabbatar da adalci.