Labaran YauNEWS

Dokan Hana Zirga-zirga A Jihar Yobe

Dokan Hana Zirga-zirga A Jihar Yobe

Gwamnan jihar Yobe, Mai Mala Buni, ya bayar da umurnin rage dokar takaita zirga-zirgar jama’a da ababen hawa na dare a fadin jihar.

Gwamnan ya bayar da umurnin ta hanyar mai taimaka masa kan harkokin tsaro, Birgediya Janar Dahiru Abdusalam (ritaya) tare da bayyana cewa matakin ya zo ne sakamakon ci gaban zaman lafiya a jihar.

DOWNLOAD ZIP/MP3

Lokutan sabuwar dokar zai fara aiki ne daga qarfe 12.00 na daren yau (Litinin) sabanin wanda aka saba; qarfe 11.00 na daren zuwa qarfe 6.00 na asuba.

Har ila yau kuma, wannan umurnin bai shafi dakatar da zirga-zurgar ababen hawa daga wannnan karamar hukuma zuwa wancan ba (ga mashin mai taya biyu ba).

A hannu guda kuma, shima zirga-zurgar abin hawa a shingayen binciken ababen hawa na jami’an tsaro zai kasance kamar yadda yake a da.

Gwamnan ya bukaci al’ummar Muslim wadanda suke da niyar halartar wuraren sallar Tahajud a wannan wata na Ramadan, za su ci gaba da gudanar da ayyukan su.

Haka zalika kuma, jami’an tsaro sun bukaci jama’a su kula da wannan canjin.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button