Labaran Yau

Mai Safaran Mota Ya kashe Jami’in Kwastom A Kebbi

Mai Safaran Mota Ya kashe Jami’in Kwastom A Kebbi

Hukumar kwastom ta kasa na ofishin jihar Kebbi ya tabbatar da kisan daya daga cikin jami’in su Aminu Abdullahi, a hannun wanda ake zargin Mai safaran mota ne a karamar hukumar Yauri na jihar.

Mai magana da yawun Hukumar, ASC Mubarak Mustapha ya tabbatar da hakan a Jawabin da yayi a birnin Kebbi.

Ya ce “Hukumar kwastom tayi jimamin rashin jami’insu da Kuma Ta’aziyya wa iyalen Aminu Abdullahi wanda ya kasance ya mutu ta sanadiyar kisa hannun mai safaran mota a bakin aikin da.

“Ya faru ranan 13 ga watan Yuli, da karfe 4 na safiya. mota kirar toyota corolla na 2015, Tana dauke chassis lamba 2TBURHE3FC456204 wanda ta bige jami’in a hanyar Tamac, karamar hukumar Yauri na Jihar.”

Yace an kai jami’in janar hospital na Yauri, domin ya samu kula daga Malam lafiya, bayan matakin daukin First Aid da ya samu.

“Daga baya a canza mai asibiti zuwa Wammako Orthopedic hospital a karamar hukumar wammako na jihar sokoto.

“Allah ya dau ransa da Safiya bayan ya samu kula a asibiti cikin dare” Cewar sa.

Mubarak Yayi addua wa jami’in wajen Allah ya jikansa da rahma da Kuma iyalensa Kan cewar Allah ya basu ikon hakuri.

Mai magana da yawun Hukumar yace an kama wanda ya kadeshi mai Suna Abdulwasiu Salawudeen, da Kuma motar  wanda suke babban ofishin dan bincike.

“Area kwantrola Dakta Ben Oramalugo ya jaddada cewa jami’an su zama masu kishin juna Kuma su zama yan uwa aikin kwastom, Kuma suyi kokari wajen bayyana bayanai na tsaro wa juna su.” Ya kara fada.

NAN

Join Our:  WhatsApp Group  |  Telegram

Watch African Stories

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button