NEWSLabaran YauPolitics

Dalilan Da Suka Saka Sen Rabiu Musa Kwankwaso Ficewa Daga Jamiyyar Lema

Dalilan Da Suka Saka Sen Rabiu Musa Kwankwaso Ficewa Daga Jamiyyar Lema

A jiya Talata ne Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya ayyana ficewarshi daga jam’iyyar PDP Lema  zuwa jam’iyyar NNPP a hukumance. Bayan shafe kwanaki da aka yi ana rade-radin Kwankwanso zai tsallaka kwalta, sakamakon shelantawa da tafiyar TNM ta yi na amincewa da akidar jam’iyyar NNPP a siyasance.

Kwankwaso wanda dan takarar jam’iyyar PDP ne a zaben shekarar 2019 ya mika wa shugabannin PDP din matsayarsa na ficewa daga jam’iyyar a rubuce, inda ya karbi katin jam’iyyar NNPP a hannun shugaban mazabar da Kwankwason yake a Abuja.

DOWNLOAD ZIP/MP3

“An yi taron jam’iyyar PDP a watan Afrilun shekarar da ta gabata, inda dukkan jihohi aka basu mukaman jam’iyya; sannan aka baiwa shugabannin jam’iyya damar tsai da wanda suke so, amma a nan Kano wasu suna ganin ban kai su bani irin wannan damar ba, don haka sai suka yi gaban kansu.” inji Kwankwaso

Ya kara da cewa: kusan shekara daya kenan ina jiran jam’iyyar ta yi min bayanin da ya dace, har aka sauya tsarin shugabancin jam’iyyar, amma babu wanda ya neme ni, na lura ba sa bukatar yin magana da ni.

Kwankwaso ya bayyana cewa wannan dalilin shine abinda ya wajabta mishi ficewa daga PDP, kuma yana ganin matakin shine mafi dacewa duba da halin ko-in-kula da uwar jam’iyyar ta nuna mishi duk da cewa shi jigo ne a jam’iyyar.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button