Labaran YauNEWS

Bincike- Alummar Jihar Plateau Na Fama Da Rashin Kulawa A Asibitin Koyarwa Dake Jos Saboda Su Hausa/Fulani Ne

Bincike- Majinyata A Jihar Plateau Na Fama Da Rashin Kulawa A Asibitin Koyarwa Dake Jos Saboda Su Hausa/Fulani Ne.

 

Majinyata Jihar  Plateau na fama da bangaranci daga likitici da wasu maaikata dake aiki a asibitin koyarwa dake jos jihar Plateau.

Bincike tare da hira da mukayi da wasu majinyata, ya tabbatar da zargin da aka jima anayi akan irin ko inkula da likitoci keyi wa marasa lafiya wanda suka kasance hausawa ko fulani.

Abun bai tsaya anan ba takaiga idan kanaso aduba lafiyanka sai ka chanza sunan yankin daka fito ko ma jiharka.

A hirarmu da malama aisha ta tabbarmana da cewa akwae lokacin da tazo asibitin, don aduba lafiyanta, a wannan lokacin wani yazo yake bata shawaran chanza sunan garinta don gudun kar a barta cikin jinya ba kulawa, haka kuwa ta amince a cewar a lokacin lafiyanta take bukata ba suna gari ba.

Saidai Ta Bangaren asibitin sun musanta wannan zargi da akeyi.

Join Our:  WhatsApp Group  |  Telegram

Watch African Stories

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button