Labaran YauNEWS

Dan Takarar Majalisar Da Hukumar EFCC Tayi Nasarar Chapkeshi Da Makuden Kudi

Hukumar EFCC tayi nasarar kama ɗan takarar majalisa ɗauke da naira miliyan 326, zunzurtun kudi da kuma dala 610,500.

Hukumar yaƙi da cin hanci da yi wa tattalin arziƙin ƙasa zagon ƙasa (EFCC) ta gurfanar da ɗan takarar majalisar dokokin jihar Kogi wanda yake takarar sa a jam’iyyar NNPP

Tuni aka maka shi a kotu hakan ya biyo bayan kama ɗan takarar mai suna Ismaila Yusuf Atumeyi da tsabar kuɗi naira miliyan 326 da kuma dalar Amurka 140,500.

Mai magana da yawun hukumar ta EFCC Wilson Uwujaren ya ce sun kama Atumeyi, wanda ke takarar ɗan majalisa mai wakiltar gundumar Ankpa 11 ne a ranar Lahadi, 30 ga watan Oktoba, 2022.

Ya kuma ce sun samu nasarar kama wani mai suna Joshua Dominic, wanda ake zargi da zamba, a lokacin wani samame da suka kai a yankin Karsana, da ke unguwar Gwarimpa, na birnin tarayya, Abuja

Ya ƙara da cewa hukumar ta kuma kama wani tsohon ma’aikacin banki mai suna Abdulmalik Salau Femi, bisa hannu a zargin na zamba, wanda ake zargin shi ne ya ƙyanƙyasa wa masu aikata zambar bayanan da suka ba su nasarar kai hari kan wani banki.

Ya ce an bincike gidan Abdulmalik, inda aka gano kuɗi dalar Amurka 470,000.

Wilson Uwujaren ya bayyana cewar an kama waɗanda ake zargin ne bayan kwashe watanni ana yin bincike game da kutsen da wasu gungun masu zamba suka yi wa wani banki.

Ya ce ana zargin masu zambar sun zare kuɗi naira miliyan 887 waɗanda suka tura asusun ajiya na wani kamfani hada-hadar mai da gas, daga nan kuma suka tura kuɗaɗen zuwa asusun masu sana’ar musayar kuɗi daban-daban da na masu sayar da motoci, abin da ya ba su damar musanya kudin zuwa dalar Amurka, da kuma sayen motoci masu tsada.

EFCC ɗin kuma ta samu nasarar ƙwato motoci biyu masu tsada ƙirar Range Rover daga waɗanda ake zargin, kuma za a gurfanar da waɗanda ake zargin a kotu da zarar aka kammala bincike.

Uwujaren ya ce hukumar ta damu da yawaitar satar kuɗin bankuna ta intanet da kuma yadda bankunan ba su kai rahoton irin waɗannan ayyukan assha ga jami’an tsaro.

Ya ce irin wannan zai iya ƙara ƙarfafa wa masu aikata laifukan gwiwa wajen ci gaba da zamewa barazana ga cibiyoyin hada-hadar kuɗi a kasar wanda hukumar ke kokarin dagile hakan.

Ga Hotunan

 

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button