Labaran Yau

Ministoti: Fadar Shugaban kasa Ta Fasa kwai

Ministoti: Fadar Shugaban kasa Ta Fasa kwai Kan Zaben Ministotin Da Zasuyi Aiki Karkashin Mulkin Bola Ahmed Tinubu Wajen Gudanar Da kasa

Ministoti: Fadar Shugaban kasa Ta Fasa kwai

Fadar shugaban kasa sun ce shugaban kasa Bola Tinubu zai sake sunayen ministoti da zasuyi aiki a karkashin gwamnatin shi lokacin da ya shirya.

Daidai da yanda dokan kasa ta tsara, Shugaban kasa da gwamnoni zasu fitar da sunanyen kwamishinoni da ministoti a cikin kwana sittin da shiga Ofishin mulki. Tinubu ya karbi karagar mulki ran 29 ga watan mayu a shekarar 2023, wanda yana da kasa da wata daya wurin bayyana ministotin sa.

Akwai rahoto akan wasu da zasu iya shiga jadawalin shugaban kasa na ministoti.

A labarin da aka samu a manyan kafafen labarai, wasu sunayen sun fito wanda ake tunanin su ne Tinubu ya ke so.

Tokubo Abiro, sanatan gabacin Lagos, da Farfesa Ali Pate, tsohon ministan lafiya wanda ya Ki amsan mukami na duniya. An samu rahoton zai iya samun Ministan lafiya.

A bayanin wani rahoto, Abiru, Tsohon Shugaban Polaris Bank, an rubuta sunan shi a matsayin ministan kudade. Ali Pate Kuma na lafiya.

A Jawabin da akayi a Fadar gwamnati ranan Alhamis, Dele Alake yace wannan rahoton an kirkiro ne kawai.

“Akan sunayen ministoti, gaskiyar magana shine wannan shugaban kasa ne na Tsarin Presidential ba na Parliamentary ba.

“Shi shugaban kasa, shi kadai zai iya fadan yaushe zai fitar da sunayen ministoti a lokacin da yakeso.

“Mun san Duk maganganun da ake kirkira a media, ni dan media ne, nasan yadda ake yi a siyar da mutum a media da kirkiro bayanai.

“Zan iya fada cewa Duk abinda ake karantawa a media an kirkiro ne. Kuma babu alaman Gaskiya akan ko daya daga ciki. Lokacin da shugaban kasa ya shirya ku zaku fara Sani”.

Kamin Tinubu ya shiga ofishin, Alake yana daga cikin kwamitin tsare tsare yace wata daya yayi wajen zaben ministoti.

“bai dauki Asiwaju fiye da sati uku ba ya zabi kwamishinoni lokacin da yazama gwamna, Ina tunanin kwana 60 Yayi yawa, wata daya in yayi yawa ayi abinda yakamata in dai gwamnati tayi serious wajen zaben ministotin ta bayan anyi rantsuwa”.  A cewar sa.

Daraktan Zantarwa na Jam’iyyar APC Bayo Onanuga ya bada tabbacin cewa ministotin Tinubu za a hadasu cikin watan da akayi rantsuwa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button