Labaran YauNEWS

Yau Shekaru 15 Kenan Da Kisan Gilan Da Akayi Wa Sheikh Ja’afar Adam

Yau Shekaru 15 Kenan Da Kisan Gilan Da Akayi Wa Sheikh Ja’afar Adam

A ranar irin ta yau cikim wata Juma’a 13, ga watan Afrilun shekara ta 2007, wasu yan ta’adda suka kutsa cikin masallaci suka harbe fitaccen malamin addinin Musuluncin nan da ke Kano, Sheikh Ja’afar  Adam.
Yan ta’addar sun harbe Sheikh  Ja’afar a daidai lokacin da yake jan limancin sallar Asuba a Masallacinsa na Al’muntada da ke yankin Dorayi Karama, cikin Karamar Hukumar Gwale ta Jihar Kano.
Yau Laraba 13, Ga Afrilun 2022 wadda ta zo daidai da 12, ga watan Ramadana na shekarar hijira ta 1443, Malamin yake cika shekaru 15 cif da rasuwa. Sheikh  Ja’afar kafin rasuwarsa ya rasu ya bar mata biyu da yara maza da mata, cikin ‘ya’yan nasa akwai Malama Zainab Ja’afar wadda yanzu take gabatar da tafsirin Al-qur’ani mai girma a masallacinsa na Usman Bin Affa da ke Kofar Gadon Kaya, Kano.
Sauran ‘yan nasa sun hada da Malam Salim Ja’afar Mahmoud da Muhammad Ja’afar Mahmoud da Abdulamalik Ja’afar Mahmoud wanda kwanakin baya ya rasu sakamakon wani hatsarin mota da ya ritsa da shi.
Marigayi Sheikh Ja’afar Mahmoud Adam, fitaccen malamin tafsirin Al-qur’ani ne da karatuttukansa suka karade kasashen Afirka ta gamma da wasu sassan duniya da dama.
A lokacin rayuwarsa ya yi nasarar karantar da litittifan Addinin Musulunci da dama, da suka hada da tafsirin Al-qur’ani mai girma da littafin Arba’una Hadith da Kitabut-tauhid da Ummadatul- Ahkam da Ahkamul Jana’iz da littittafi masu dimbin yawa da suka shafi Al-qur’ani da Hadith da Tauhidi da Tarihi.
Sheikh  Ja’afar Mahmoud, ya rasu a tafarkin da’awa da wa’azi, inda ya koyar da daliban ilimi darussan musulunci da dama a Jihohin Kano da Maiduguri da Katsina da Bauchi da sauran garuruwa da dama da ma wasu kasashen nahiyar Afirka da dama.
Allah Addu’ar Allah ya gafarta masa, ya kyauta bayansa, ya kyauta namu zuwan.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button