Ba Alaman Sassauta Hari – Russia Da Ukraine
Rasha Ta Kara Kaimi Wajen Kai Sabbin Hari Gabashin Ukraine
A ‘yan kwanakin da suka gabata, Rasha ta jaddada cewa za ta mayar da hankali wurin kai hare-hare a gabashin Ukraine, kuma hukumomi leken asirin Birtaniya sun ce mai yiwuwa hakan “wata hanya ce ta amince cewa” tana shan wahala wajen kai hare-hare a arewacin kasar.
Kwace garuruwa da filayen da ke kudancin yankin shi ne babban burnin Shugaba Putin, da kuma bukatarsa ta “ceto” yankin gabashi. Tuni ‘yan tawayen da Rasha take mara wa baya suka kwace fiye da kashi biyu cikin uku na yankuna biyu na gabashin kasar a 2014.
Dakarun Rasha sun ci gaba da mamayar arewa maso gabashin yankin Luhansk, sai dai ba su da iko sosai kan Donetsk kuma jami’an tsaron hadin gwiwa na Ukraine da ke gabashi sun musanta cewa an kwace yankin.
Sai dai Rasha ta kara kaimi wajen kai hare-hare a garuruwan da ke yammaci.