Labaran Yau

Hukumar Kula Da Kwaya Da Miyagun Kwayoyi Na Kasa NDLEA Ta Kama Kwaya A Legas

Hukumar kula da kwaya da miyagun kwayoyi na kasa NDLEA ta kama kwaya a legas

Hukumar dokar kwaya ta kasa, NDLEA ta kama miyagun kwayoyi wanda ta kunshi tramol, rafanol, ganyen wiwi da sauransu wanda aka saka jikin rigunan sanyi da kwalaben man shafawa (body Lotion) a jihar legas.

Hakan ya bayyana daga bakin mai magana da yawun Hukumar NDLEA, Femi Baba Femi ran asabar A Abuja.

BabaFemi yace kwayoyin an kama ne a filin jirgin Murtala Muhammad ran jumma’a a jihar legas.

Yace kwayan zarewan a kama ne a sabon mashigan filin jirgin.

An kama kwayan ne a hanun wani fasinja meh suna Joshua sunday, wanda zai yi tafiya a jirgin qatar ta Doha zuwa Oman, Yankin gabas ta tsakiya.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button