Tsohon Kakakin Majalisar Jihar Kano Ya Rasu
Allah Yayiwa Tsohon shugaban majalisar Dokokin jihar Kano Hon Yusuf Abdullahi Falgore Rasuwa a safiyar yau Lahadi.
An haifeshi a garin Falgore, na karamar hukumar Rogo, Jihar Kano a Najeriya.
Yayi makarantar Falgore Central primary a shekarar 1963 – 1969 sannan ya halarci Gwarzo Senior Primary School. Daga nan ya wuce Kwalejin Malamai ta Bichi a shekarar 1970 kuma ya kammala a shekarar 1974.
Daga 1975 – 1978 ya halarci Makarantar Advance Teachers College, Zariya, ya kuma fito da takardar shaidar karatu ta kasa (NCE). Daga nan ya wuce Jami’ar Ahmadu Bello da ke Zariya (1981 – 1983) don yin digiri a fannin Ilimi.
Kafin ya shiga siyasa Yusuf Falgore ma’aikaci ne a ma’aikatar ilimi ta jihar Kano. Falgore shine tsohon kakakin majalisar Jihar kano kuma shi ne Shugaban Kwamitin Gudanarwa da Nasiha tsakanin 2011-2015 ya jagoranci Kwamitin Majalisar kan Ilimin Sakandare.
An zabi Falgore a matsayin Shugaban Karamar Hukuma batare da Jam’iyya ba, sannan ya zama Shugaban riko (Sau biyu) 1991 – 1993, 2002 – 2003 bi da bi. An zabe shi a matsayin dan Majalisar Dokoki ta Jihar kano sau biyu, 2011 – 2015 sai 2015 – 2019 bi da bi, kuma ya rike kakakin majalisar jahar kano na yan watanni kafin a tsigeshi a maye gurbinsa da Gambo Sallau a shekarar 2011.
Zaayi jana’izarsa yau Lahadi da karfe hudu na yamma a gidansa dake sharada ja’en a cikin kwaryar birnin kano.
Muna rokon Allah ya Gafarta Masa Ameen.