Dan Takarar Gwamnan Jihar kogi ya dau malamin Firami a matsayin mataimaki
Dan takarar gwamna a jam’iyyar APC Usman Ododo, ranan lahadi, ya bayyana malamin firamari Salifu Joel, a matsayin ma taimakin shi na zaben Gwamna da za ayi ran 11 ga watan nowamba.
Hukumar labarai ta kasa (NAN) ta bada rahoton cewa shi mataimakin shine ciyaman na hadakaiyar malamai na kasa Yanzu haka, Kuma ma’aji na Hukumar kwadigo na jIhar kogi.
Gwamna Yahaya Bello, wanda yayi magana a wajen taron a gidan gwamnati, yace an zabi Joel wanda malamin Makaranta ne dan yazama mataimakin Gwamna a Jam’iyyar APC, sqboda a jawo mutane kusa wanda shine burin jam’iyyar dan kawo cigaba wa jihar.
Bello ya jaddada cewar zasu jajirce dan jam’iyyar APC ta lashe zaben 11 ga watan nowamba na zaben Gwamna a jihar.
“APC zata bi dokokin zabe dan taci zaben nowamba, dan gwamnati Na ta kawo cigaba na hanyoyi, ingantaccen ilimi da kuma asibitoci da sauransu.
“Mun nuna kwarewa, jajircewa wa kogi da mutanen kogi yasa muke neman kuri’un su dan mu kawo gwamna daga jam’iyyar APC.
“Baramu yarda siyasan batanci koh siyasa mai daci ba, ko tashin hankali na siyasa, saboda jihar yafi karfin Zan san zuciya.
“Siyasar addini ko kabilanci bareyi tasiri ba a kogi. Yakamata kowa ya kama bakin sa daga kalamai mara amfani wanda zai iya kai mutum da da nasani gobe” ya ka kunne.
Ciyaman din jam’iyyar APC na jihar, Abdullahi Bello, ya taya dan takarar gwamna da mataimakin sa murna, da kuma yabawa gwamna dan ayyukan da yayi da kuma shugaban ci Mai inganci na jam’iyyar.
Ya yabawa zabin mataimakin Ododo, cewa ya zo daga wuri mai amfani a gari.
Joel yace “bani da abin fada, dan ni malamin Makaranta ne Kuma aka daukeni inyi mataimakin gwamna wa dan takarar gwamna na jam’iyyar APC.
“Lokacin da aka min magana akan batun nayi matukar murna har cikin zuciyana, na amsa da hannu biyu.
“Zan iya kokari na dan in tabbatar jam’iyyar mu taci zabe, a zaben da za ayi gwamnoni” Joel ya bada tabbaci.
NAN