
Advertisements
Yadda Ake Hada Soyayyen Kabeji
Ita Soyayyar Kabeji hadi ne zamani dan gyara nau’in abincin mu, ita kabejin da aka soya ana iya cin shi da shinkafa Jollof ko Fried, Ana iya ci da couscous ko taliya ko macaroni, da sauransu.
Advertisements
Kayan Hadi
Kabeji
Kwai
Mangyada
Maggie attaruhu
Albasa
Maggi
Gishiri
Yadda Ake Hadawa
Da farkon Za a wanke albasa da kabeji a tsantsame sai a yanka, sai a daura man gyada a sa albasa a soya idan ya soyu sai a zuba kabeji a ciki sannan sai a rufe
Bayan minti uku haka zuwa biyar sai a Bude za a ga ya Danyi ruwa, sai a kada kwai a saka attaruhu, albasa, Maggie da gishiri idan anaso aman idan ba a so ba sai an sa ba
Sai a zuba a Kai ana soyawa ana juyawa har ya soyu sai a juye a kwano aci shinkafa ko taliya ko dan wake ko couscous.
Aci Dadi lafiya

Advertisements