Labaran Yau

Da Akan Gina Masallatai Gwara A Karkatar Da Kudaden Islamiyoyi Domin…Cewar Shugaban Alphopi

Jagoran Alphopi na kasa baki daya wanda akafi sani da Qaloon Muazu ya bada shawarin cewa gwara adena gina Masallatai ayi amfani da kudaden wajen inganta salarin malaman Islamiyoyi.

A cewar sa yin hakan shi zaisa makarantun su samu kudaden shiga da fiche.

Ga cikaken bayanin yanda jami’inmu na Labaranyau ya samo ⇓

Kuɗaɗen da ake gina Masallatai dasu, in da ace ana karkatar dasu zuwa Islamiyoyi da za a iya samun kuɗin da za a riƙa biyan Malaman Islamiya fiye da abinda gwamnati take biyan Malaman Primary da Secondary.
Akwai Jami’o’i da yawa na duniya da ba Gwamnati ce take ɗaukar nauyinsu ba, kuma ba wai kuɗin makaranta ne ke riƙe su ba. Kuɗaɗe ne na Sadaka (Donations) da suke samu.
Waɗannan kuɗaɗen kuma suna da yawan da ana sanya su ne ƙarƙashin kulawar Fund Manager da yake juya kuɗin ana samun riba, kullum kuɗaɗen suna ƙaruwa.
Islamiyya School
Islamiyya School
Shiyasa irin waɗannan makarantu ba zaka taɓa samun Malamansu sun tagayyara ba. Albashin Malaman yana da kyau shiyasa suke iya samun Malaman da suka fi ƙwarewa.
Akwai kayan aiki, akwai bayan gidoji masu kyau da tsafta, yara ba zasu yi infection ba. Za a samu ilimi yadda ya kamata.
Ilimi shine ginshiƙin cigaban kowace al’uma.
A Arewa kullum muna samun Graduates daga Jami’o’in Musulunci na duniya, amma mafi yawansu ko dai su je su koyar a Islamiyar da ba a iya biyan minimum wage, ko suje su dawo yaran Ƴan siyasa da Alhazan Birni suna koyar da ƴaƴansu da sauran hidindimu na bambaɗanci da wulaƙanci, ko kuma su watsar da karatun addinin da suka koya, su je su kama wata hanyar neman kuɗin da ko da basu je Jami’ar Musulunci ba, zasu iya yin wannan abu, don haka zuwa Jami’ar Musuluncin bai yi amfanin da ya kamata ba.
Akwai wani abu da naji ƴan Brekete Family suna cewa “In za a gyara, a gyara”.

Meh zaka iya cewa dangane da wannan shawari da aka bayar akan samarda kudin shiga da fiche Islamiyoyi?

Join Our:  WhatsApp Group  |  Telegram

Watch African Stories

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button