Yadda Ake Tuwon Dawa
Tuwon dawa tuwo ne na hausawa duk da dai wasu yankin fadin kasar najeriya ma an gano suna ci, ana cin ta da miya iri iri duk wanda rai ya fi so. tuwon dawa yana saukin sarrafawa. karanta yadda ake hadawa.
Kayan Hadi
Nikeken garin dawa
Kanwa
Ruwa
Yadda Ake Hadawa
Da farko zaki dora tukunyarki a wuta ki sa ruwa daidai misali
Idan ya tafasa sai ki debo garin dawarki da ki ka tankade kisa ruwa ki dama ki zuba a kan tafasasshen ruwan.
Sai ki sa mucciya ki juya don kar ya yi gudaje. Sai ki kawo ruwan kanwa kadan ki zuba ki barshi yayi ta dahuwa.
Idan yayi sai ki tuka zaki ga har yauki yake yi. Idan kin gama tukawa sai ki rufe ya dan turara, zaki ji yana kamshi sai ki malmala.
Zaki iya cin tuwon dawa da irin miyar da ki ke so, amma yafi tafiya da miyar kuka ko danyen kubewa.