Yadda Ake Miyar Waken Suya
Miyar waken suya miya ce wanda aka fi ci a kudancin kasar najeriya. a saukake ga yadda ake hada miyar waken suya (Soya Beans soup).
Kayan Hadi
waken suya
tumatur
ataruhu
albasa
ganyen albasa
maggi
manja
citta
alayyahu
Yadda Zaki Hada
Ki sami waken suyan ki ki tsinceta ki gyara, sai ki jika kamar na minti 15 kikai amarka da miki idan adawo daga kai markade, dama kinada kayan hadin da aka kissafa, sai ki soya manjanki daga nan sai ki zuba markadaden kayan miya sai ki rufe idan ya soyu sai ki zuba wannan markaden waken suyan akai. Ki rufe miti goma zuwa shabiyar sai kizuba ganyenki na alayyahu da ganyen albasa.
kina iya ci da tuwon semo, ko na gari ko tuwon shinkafa ko sakwara.
Ba,a tace markaden waken suyan, kuma wannan miyar tana da auki sosai.