Girke Girke

Yadda Ake Sarrafa Funkaso

Yadda Ake Sarrafa Funkaso

Ita Funkaso abu ne mai dadi da saukin sarrafa wa, biyomu kadan dan ganin yadda muke sarrafa ita funkaso

Abubuwan Hadawa

Fulawa
Yeast
Gishiri
Man gyada

Yadda Ake Hadawa

1.Dafarko zaki tankade fulawarki ki sa gishiri kadan sai ki ajiye a gefe.

2.Dauko yeast na ki, ki sa masa ruwan dumi ba me zafi ba da suga karamin cokali daya ki juya, sai ki rufe ki ajiye a gefe kamar na tsawon minti biyar, idan ya na da kyau za ki ga ya yi kumfa ya kumbura amfanin yin hakan don ki san yeast din mai kyau ne.

4.Sai ki juye yeast din cikin filawanki kidan kara ruwa ki kwaba shi kamar kwabin fanke sai ki rufe ki kai rana ya tashi Kamar minti 20-30 idan ya taso sai ki kara buga shi sosai ki ajiye a gefe.

4.Ki dauko kasko ki daura kan wuta, ki zuba man gyada idan ya yi zafi, sai ki na diban kwabin funkasau nan kadan kadan ki na fadada shi da hannunki ki na sawa a mai ki na soyawa har sai ya soyu, sai ki tsane a matsani. Ana iya cin funkasau da miyan stew, miyan taushe, Ko miyar ganye.

Sarrafaffiyar Funkaso
Sarrafaffiyar Funkaso

A ci dadi lafiya.

 

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button