Girke Girke

Yanda Ake Gwaten Filanten, Soyayyen Plantain Da Kwai

Gwaten Filanten Mafi yawan lokuta amfani jin dadin plantain idan aka soya shi, ko a tafasa shi ko a gasa shi a ci da sauce. Paten Plantain Yana da dadi da kuma sauki wajen hadawa.

Ita wannan abinci anfi ci kudancin Najeriya.

Kayan Hadi

  • Danyen Plantain
  • Nunannen Plantain
  • Kabewa
  • Alaiyaho
  • Albasa
  • Crayfish
  • Manja
  • Maggi
  • Busashshen Kifi
  • Nama
  • Attaruhu
  • Tattasai

Yadda Ake Hada Gwaten Plantain

  • Da farko za a wanke a fere plantain, kamin nan an saka nama a wuta dan ya tafasa da kayan kanshi za’a jirashi har sai naman yayi laushi.
  • Sannan a yanka plantain daidai girman da ake so ayi amfani dashi, sai a saka a wuta a zuba manja, attaruhu, crayfish, maggi da gishiri kadan.
  • Sai a barshi ya dahu na Dan wani lokaci, sai a zuba busashshen kifin sai a juya shi da ludayi.
  • Sai a zuba Alaiyahu a barshi yayi minti biyar.
  • Sannan a sauke.

Soyayyen Filanten Da Kwai (Fried Plantain with eggs)

Shi wannan abinci na marmari ne Wanda akeci a duk fadin najeriya. Daga gidaje har wajen siyar da abinci anayi kuma Yana da saukin hadawa ga marasa aure.

Kayan Hadi

  • Plantain Nunanne
  • Koyi guda daya
  • Piya
  • Man gyada
  • Gishiri

Yadda Ake Hada Soyayyen Plantain Da Kwai

  • Da farko za a fere plantain sai a yanka, sai a Dan watsa Gishiri kadan a kan plantain din da aka yanka.
  • Sai sanya frying pan akan wuta a zuba mangyada, in yayi zafi sai a zuba plaintain a ciki sai a rage zafin wutan kadan Dan ya soyu da kyau.
  • Har sai yayi jajawur kamin a sauke.
  • Sai a fasa kwai a cikin dan karamin kwano
  • A yanka albasa da attaruhu ciki in Ana bukata da dan maggi. A kada da kyau
  • A sanya frying pan a wuta a zuba man gyada cokali daya ko rabin cokali in yayi zafi sannan a zuba kwan a soyashi da kyau.
  • Sai a zuba plantain din da aka soya a plate, a saka soyayyen kwan a cikin plate din sai a gyara piya shima a saka a shirya shi.

Yanda Ake Asillen Kwadon Zogale

Join Our:  WhatsApp Group  |  Telegram

Watch African Stories

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button