Ita Okpa abinci ne wanda akeyi da gurjiya, kuma mafi yawa Inyamurai(Kabilar Igbo) suka fi cinta a kudancin kasar najeriya. Ko da yake wasu daga cikin hausawa da yarbawa ma suna Jindadin ita Okpa.
Kayan Hadi
Kofi hudu Na Gurjiya
Attaruhu na 50 naira
Ogiri
Maggi 1
Gishiri
Manja rabin kofi ko gwangwani daya
Yadda Ake Hadawa
Da farko ake wanke gurjiya a surfe, sai a markada da attaruhu. Sannan a zuba maggi da gishiri kadan, in an juya sai a zuba manja.
A juya da ludayi har sai ya bi jikin markaden sannan a zuba a cikin laida a daura.
A samu tukunya a zuba ganye a ciki, Sannan a zuba ruwa. In yayi zafi sai a saka alalen da aka daura a wuta.
In ya dahu sai a sauke
Wasu suna ci da gishiri wasu sukan ci da yacin barkono.