Yadda Ake Banana Milkshake
Kayan Hadi
Banana (ayaba) guda biyu manya
Sugar cokali biyar
Madara cokali goma
Ice block (kankara)pure water biyu
Yadda Zaki Hada
Za’a yayyanka banana asaka a blender sai a zuba sugar da Madara asa kankara a ciki idan blender din bayi da karfin markada kankara a saka kankaran a turmi a rage masa karfi sai a saka a cikin blender a markada ya zama creamy yayi smooth kaman de ice cream sai a juye a cup asaka straw asha baya daukan lokaci cikin minti biyu zakiyi komi ga dadi.
Lemon Kankana Cikin Minti Biyu
Lemun kankana yana da matukar amfani a jikin dan adam musamman masu ciki, yara da magidanta.
Wasu lokutan ma akan ce kankana yana karawa yara kyau.
Yana kara ruwan jiki Kuma yana taimakawa wajen kara karfin garkuwan jiki. Cikin kankanin lokaci Zamu sarrafa wannan lemun kankana.
Kayan Hadi
Kankana na 100naira
Citta (ginger) na 50naira
Dabino na 50 naira
Ruwa Kofi daya da rabi
Yadda Ake Hadawa
Za a yanka kankana kanana, Sai a wanke danyen citta, a wanke dabino a cire kwallon Sai a zuba a cikin blender, a zuba ruwan Sai a markada yayi laushi sosai.
Sai a tace shi da matata ko karamin siever, sannan a kara sugar ko da cokali dayane. In ana son madara ma za a iya sakawa da kwallon kankara kanana guda biyu.
Sai a zuba kofi asha lemo mai Dadi.
Yadda Ake Hada Lemon Cucumber
Lemun cucumber yanada matukar dadi da Kuma sauki wajen hadawa, shan ire iren wannan lemo yafi amfani akan lemon kamfani saboda sinadaren da ake zubawa.
Kayan Hadi
Cucumber Guda daya babba
Citta danye guda biyar
Lemun tsami biyu
Sugar Cokali biyu
Ruwa kofi uku
Yadda Ake Hadawa
Idan za a fara, Sai a wanke cucumber a yanka into small pieces, kanana Sai a zuba a cikin blender tare da danyen citta.
Sannan a markada yayi laushi ayi sieving da matata. A juye cikin kwano Sai a matse lemur tsami a sanya sugar a gauraya sosai.
A saka a fridge yayi sanyi asha.