Addini

Falalar Azumin Nafila 

Falalar Azumin Nafila 

Hadisi ya inganta a sunani nasa’i, hadisi na 2360. Nana Aisha RA Allah ya kara yadda da ita, Manzon Allah SWA ya kasance yana kirdadan Azumi ranar Alhamis da litinin.

Wanda a wasu hadisai ya nuna mana dalilin azumin sa a ranar litinin , shine saboda a ranar ne aka haifeshi kuma aka saukar masa da alqurani, Ana kuma kai dukkan aikin duk wani musulmi ranar Alhamis da ranar litinin, shi yasa yake Azumin alhamis da litinin, kayi kokari kayi Azumi Saboda bakasan yaushe zaka mutu ba. Zaifi kyau Allah ya dau ranka kana Ibadar Azumin nafila.

Mu sani cewa azumi ita ke nesantar da mutum daga wuta tafiyar shekaru 70, kuma ita kadai ce aikin da Allah yace nashi ne, kuma shi kadai zai biya ladan Azumi. Daga cikin abin da Azumi ke koyarwa shine hakuri, Allah Yana sakankawa masu hakuri ba tare da kididdiga ba.

Sunnah ta so ka da Azumin nafila guda uku a wata, ka samu ranar 13, 14 da 15 na kowata wata na kirgen musulunci. In bahaka ba na Alhamis da litinin, ko ba haka ba anaso yau kayi azumi gobe kaci ainihin abinci. To wannan tana daga cikin abin da shariah ta so.

Sannan shariah ta kwadaitar game da Azumin sha’aban. Sai dai zaka iya azumtar watan gaba daya, zaka iya axumtar mafi yawan cin shi, Abinda aka kyamata shine kaki fara Azumin tun a 15 na farko, sai a 15 na karshe, to an kyamace wannan. Sai Azumin hawan Arfa, Ana so lallai kayi azumin Arfa in kana da iko, domin mustahabbi ne.

Sai dukkan wadannan azumummuka idan sunyi karo da ranar asabar to shariar musulunci ta hana. Ba a azumin nafila ranar asabar, kuma da azumi 6 bayan ramadana. Azumin watan shawwal sunnah ce tazo a sahih Muslim. Zaka iya yi bayan watan Ramadan ko ana binka bashi (ma’ana inkinyi haila) ana binki kwana uku, toh ana jinkirtashi ayi sitta shawwal.

Kalli bidiyon a kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button