Binani: Wasu daga cikin dalilan da yasa mace barata iya mulki ba ta idon addini
Ni dai Adamawa ina bayan Namiji bana bayan Mace. Domin haramunne mace ta zama itace saman kowa.
1. Zata iya cire sarki ta naɗa wani
2. yan majilisu basu isa su zartar ba sai ta gadaman sa hannu
3. idan ta haihu yaya za ayi da rainon ciki da goyo
4. Idan mijinta ya mutu ina labarin zaman takaba na wata 4 da kwana 10?
5. A musulunci miji na saman matarsa, da zata ɓata masa rai yace ba za ta je wani taro ba yaya abun zai kasance idan taron ya zama dole?
1. Ba a taɓa mace Annabiya ba
2. Sahabbai guda huɗu da suka fi kowa duk mazane
3. ba a taɓa tura mace da tutar yaƙi ta jagoranci maza a zamanin Annabi ba
Da kayi magana sai wani yace ai ba mulkin musulunci ake ba, to kenan musulmi basa karkashin mulkin nan? Basa bin dokar ƙasar nan?
Gamnan garinmu Elrufa’i yayi aniyar tsayar da mace takara, sai ya tara malamai yace ya matsayin haka a Addinin musulunci? Malamai suka ce haramunne, dama dama tayi Senato ko yar majalisa.
Malamai sunce idan Arne ya tsaya takara da musulma, to anan hani biyu sun haɗu, amma zaɓan mace yafi zaɓen kafiri. To Adamawa dai musulmi da musulmace, haramun ne kana Ba’adame ka zaɓi Mace.
Malam Geenty ya rubuto