Labaran Yau

Dino Melaye Ya Siya Tikitin Takarar Gwamnan Jihar Kogi A Jam’iyyar..

Dino Melaye ya siya tikitin Takarar gwamnan jihar kogi a jam’iyyar PDP

Dino Melaye, tsohon sanatan kogi ta yamma, ya bayyana cewa shi yaci zaben firamari na takarar gwamna a jam’iyyar PDP.

Hukumar labarai ta kasa ta bayyana sakamakon zaben wanda Dino ya samu kuri’u 313 ya lashe zaben har yakai da kada dan takara Idoko Ilonah wanda yasamu kuri’u 124 a zaben da akayi ran lahadi a lokoja.

Shugaban zaben firamari na PDP, Ahmed Makarfi Yace zaben anyi ne cikin kwanciyan hankali da zaman lafiya.

Makarfi yace sauran yan takarun kamar su Mohammed kabiru wanda ya samu 121 da Aboyomi Awoniyi sunday ya samu 77 Sai wada musa ya samu 56.

A bayanin shi, Ojaja Gideon Enama wanda yasamu kuri’u biyar da olufemi olarewaju ya samu biyu. Kuma kuri’u shida ne kawai suka baci.

Yanawa dino Melaye murnan lashe zaben firamari wanda ya kasance shine dan takarar jam’iyyar PDP a jihar kogi.

Yayi godiya wa mambobin jam’iyyar wurin kokari dan ayi zaben cikin lafiya koshin lafiya a yanda daily Nigeria ta rawaito.

Join Our:  WhatsApp Group  |  Telegram

Watch African Stories

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button