Labaran Yau

NAFDAC: Taliyar Indomie Na Najeriya Tana Ciwuwa

NAFDAC: Taliyar Indomie na Najeriya tana ciwuwa

Hukumar kula da abinci da kwayoyi na kasa NAFDAC tace taliyar indomie wanda akeyi a Najeriya batada alaka da wanda akeyi a kasar Malaysia da Taiwan.

Hukumar tace taliyar da akeyi ta indomie a Najeriya bata da wata matsala Kuma Tana iya ciwuwa.

Indomie Noodles

DOWNLOAD ZIP/MP3

Darakta Janar na Hukumar Mojisola Adeyeye ta bayyana a gidan talabijan na TVC cewa taliyar indomie, gwamnatin tarayya ta jima da hana shigowa da su Najeriya, kuma Suna daga cikin jadawalin customs na abincin da aka haramta shigowansu. Saboda a taimaka wajen tada kampanin da suke iya yin wannan taliyar da kuma inganta tattalin arzikin kasa.

Hukumar tace Tana kokarin magance duk wata kofa da zai sa a shigo da irin wannan abincin a kasa ko Kuma toshe hanyar da za a shigo da ire iren abincin da muke iya yi da kan mu.

Wanda hakan yasa hukumar ta bude dakunan bincike da yin aiki tukuru dan binciko abincin da suke iya haifar da matsala wa jikin dan Najeriya.

A bayanin manajan Prima Foods Plc, ya ce “indomie da akeyi a Najeriya daban ne da wanda akeyi a Malaysia da Taiwan. Kuma indomie da akeyi a Najeriya yakai shekaru 30. Dufil Prima Tana kokarin bunkasa hada abinci dan ya ishe jama’a, da ace an dogara da shigowar su daga kasashen duniya”.

Najeriya Tana daga cikin masu cin taliyar indomie sosai Kuma hakan yasa taliyar ta ke ko wata kasuwa a kasar.

Najeriya tafi ko Ina cin taliyar indomie da masu ci sama da mutum miliyan 1.92. Haramcin shigowar taliyar daga wasu kasashen cigaba ne wanda Ya jima a haramtaccen abinci a jadawalin Gwamnatin Tarayya.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button